ECOWAS na ci gaba da kokarin shawo kan Jammeh | BATUTUWA | DW | 09.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

ECOWAS na ci gaba da kokarin shawo kan Jammeh

A kokarinsu na neman kauce wa tashin hankali a Gambiya, shugabannin kasashen yankin yammacin Africa na shirin sake komawa birnin Banjul a ranar Laraba domin ganawa da shugaba Yahaya Jammeh da nufin matsa masa lamba.

Lokaci mika mulkin Gambiya na kara karatowa sannu a hankali, sannan rudani na kara yawa a cikin rikicin siyasarta saboda tana shirin samun shugabanni har guda biyu. Abiin da kasashen yankin yammacin Afirka suka yi kokarin kaucewa, a wani taron koli na shugabbanin kasashen guda hudu masu shiga tsakanin bangarorin guda Biyu.

Shugabannin da suka hada da Buhari da Sirlief ta Laberia da ke shugabantar ECOWAS da kuma Koroma na Saliyo da Mahama da ya bar gado a Ghana sun yanke hukuncin sake daukar hanyar zuwa Banjul a ranar Larabar da ke tafe domin dorawa a kokarin neman mafita.

Bayan taron na Abuja dai, kasashen yankin sun damu da zaman dardar din dake dada karuwa a cikin yankin yanzu.

Senegal Proteste gegen Nicht-Anerkennung der Wahl in Gambia
(Getty images/AFP/Seyllou)

'Yan Gambiya na nuna damuwa kan halin da ake ciki

 Duk da cewa kasashen ECOWAS ko CEDEAOsun bayyanna aniyarsu na daukar matakai na kare kundin tsarin mulkin Gambiya, sun yi shiru ga yiwuwar amfanin da karfin tuwo da sannu a hankali ke kara fitowa a matsayin zabin karshe.  Akwai dai rahotannin yiwuwar daukar sojojin haya daga makwabtan Laberiya da Côte Ivore a bangaren Jammeh da har yanzu ke da goyon bayan soja.

A ranar 19 ga watan Janairun 2017 ne ake tsara mika mulki ga sabon shugaban kasar Adama Barrow a wani bikin da daukacin shugabannin kasashen ECOWAS ko CEDEAO suka sha alwashin halarta.

 

Sauti da bidiyo akan labarin