Ebola ta zama barazana ga duniya | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 01.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Ebola ta zama barazana ga duniya

Annobar cutar Ebola da matsalar kungiyar Boko Haram sun addabi yankin yammacin Afirka da ma duniya baki daya

Symbolbild Ebola Westafrika

Yaki da Ebola

Sharhunan jaridun Jamus a wannan mako sunfi mayar da hankali ne kan annobar cutar Ebola, wanda yanzu ta ke kara daga hankalin duniya. Jaridar Frankfurter Algermeine Zeitung, ta fara labarinta da cewa. Likita na biyu ya rasu bisa cutar Ebola. A kasar Birtaniya a karon farko an samu wani likita da ya fito daga yammacin Afirka yana dauke da wannan cutar. Jaridar ta ce, sakataren harkokin wajen Birtaniya Philip Hammond ya fadi cewa yanzu cutar ta Ebola ta kasance wata babbar barazana ga duniya baki daya. A yanzu dai kungiyar Tarayyar Turai ta ware Euro miliyan biyu domin yaki da cutar ta EBola.

Ita ma jaridar Süddeutsche Zeitung, ta yi sharhinta ne kan cutar ta Ebola, inda jarida ta fara da cewa an kaddamar da dokar ta baci kan cutar Ebola a Yammacin Afirka. A yayin da kungiyar lafiya ta duniya WHO ke cewa, tun barkewar annobar Ebola, yanzu mutane 726 suka mutu a kasashen Gini, Laberiya da Saliyo. Don haka jaridar ta ce a yanzu dukkan kasashen yankin sun kaddamar da wani sabon mataki na yaki da bazuwar cutar a kan iyakokinsu. Kasar Saliyo ita ce ta fi fiskantar wannan matsalar a yanzu, inda kuma shugaban kasar Ernest Bai Koroma, ya sanar da kafa dokar ta-baci kan yaki da cutar Ebola.

Kamerun Soldaten gegen Boko Haram

Sojojin Kamaru a bakin daga

Sai Jaridar Neue Zürcher Zeitung, wanda ta yi tsokaci kan kungiyar Boko Haram. Jaridar ta ce Boko Haram yanzu basu da kan iyaka. Kungiyar kan kaddamar da hari a inda ta ga dama cikin har da makobata kamar kasar Kamaru, inda suka kai wani hari, kana suka sace wasu 'yan siyasa biyu. Bayan harin jaridar ta ce shugaban kasar kamaru Paul Biya ya nada kwamandojin jami'an tsaro, domin su yaki kungiyar Boko Haram. Bisa yakin dai yanzu gwamnantin Kamaru ta tura wata rundunar jandarma da bataliyar soji. Wannan dai ya biyo bayan sukar da ake yi wa gwamnati, da ce Paul Biya ya yi biris da hatsarin da mutanen Arewacin kasar ke fiskanta bisa harin kungyar Boko Haram.

Ita kuwa jaridar die Tageszeitung, ta yi waiwaye ne kan harin da aka kai a Kaduna. Inda jaridar ta ce rikicin ta'addacin yanzu ya koma wata kazamar siyasa. Harin da aka kai wa fitaccen malamin addinin Islama Sheikh Dahiru Usman Bauchi da jagoranm adawan kasar Janar Muhammadu Buhari, ba wai hari ne da aka kai a kasuwa ba, domin ada 'yan kungiyar sukan kai hari ne kan tashoshin mota da kasuwanni, amma an kai shi kan wadannan fitattun muta ne na arewacin Najeriya. Ko da yake duk Sheikh Dahiru Usman Bauchi da Janar Buhari, babu wanda ya ji ko kwarzone a hare-haren, amma akalla mutane 80 suka mutu, wasu da-dama suka jikkata, kuma cewar jaridar wadannan hare hare biyu da akai a Kaduna kusan loka ci guda a rana guda, to dole za su zame wa shugaba Goodluck Jonathan wani karfen kafa.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Zainab Mohammed Abubakar