Wani ya sake kamuwa da Ebola a Kwango
April 10, 2020Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce an sake samun wani mutun dauke da cutar Ebola a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango a wannan Juma'a a daidai lokacin da ya rage kwanaki uku Hukumar Lafiyar ta duniya ta ayyana kawo karshen annobar cutar ta Ebola a hakumance.
Daraktan hukumar ta WHO ko OMS Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya sanar da wannan labari a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tweeter a wannan Juma'a inda ya ce wannan na nufin assalatu ta warware a game da shirye-shiryen da ake na ayyana kawo karshen wannan Annoba ta Ebola a Jamhuriyar Dimukuradiyyar kwango.
Ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Kwango Kinshasar ta bayyana cewa mutuman da aka sake samu da cutar ta Ebola wani matashi ne dan shekaru 26 mazaunin birnin Beni. Wannan dai shi ne mutun na farko da aka sake samu dauke da cutar ta Ebola a cikin kusan watanni biyu na baya bayan nan.