Ebola ta kawo fatara a Saliyio | Labarai | DW | 27.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ebola ta kawo fatara a Saliyio

Hukumar abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya FAO ta ce a yankunan da cutar Ebola ta ɓulla a ƙasar ana fama da matsala ta ƙaranci abinci,

A wani binciken da ta gudanar hukumar ta ce a cikin kishi ɗari, kishi 70 na jama'ar da aka yi wa tambayoyin sun ce sau ɗaya suke cikin abinci a yini.

Darakatan hukumar da ke ƙokarin shawo kan cutar ta Ebola Martin Vincent,wanda hukumarsa ta gudanar da bincike na haɗin gwiwa tare da hukomin PAM da na FAO.Ya ce fatara da manoma ke fama da ita, ta janyo musu cikas wajen yin aikin noman, don haka dole sai an taimaka musu domin su sake farfaɗowa.