Ebola na ci-gaba da yaduwa | Labarai | DW | 10.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ebola na ci-gaba da yaduwa

Duk da irin nasarar da aka samu kan yakar cutar Ebola, masana sun yi gargadin har yanzu annobar na kara bazuwa a wasu yankunan

Babban jami'in MDD kan cutar Ebola, David Nabarro, ya yi gargadin cewa har yanzu cutar na ci gaba da yaduwa a kasashen Saliyo da Gini. Jami'in ya kuma yaba da yadda aka samu ci-gaba wajen yakar cutar a wasu kasashen yammacin Afirka. Ya kara da cewa ana matukar bukatar karin kwararrun likitoci da gadajen kwantar da marasa lafiya, a yankunanan da annobar cutar Ebola ta shafa. Nabarro ya furta hakanne yayinda ya ke wa manema labarai jawabi, a ofishin MDD da ke Geneva. Inda yace ba za mu zauna ba, wai mu ce mun kusan kammala aikin, domin kawai yanzu mun tantance yankunan da cutar ta riga ta kama, in mun yi haka cutar na iya tsallakawa a yankunan da ba su kamu. Sabo da gudun kada ya kai ga inda ba'a taba samun cutar ba, a kullum mukan wayi gari da tunanin jan aiki da ke gabanmu. Shugabar kasar Laberiya Ellen Johnson Sirleaf ta kaddamar da wani shirin da aka yi lakabi "Ebola Must Go" wato dole mu kori Ebola.