Ebola na bukatar taron dangi na gaggawa a cewar Amurka | Labarai | DW | 23.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ebola na bukatar taron dangi na gaggawa a cewar Amurka

Rashin samun cikakkun bayanai na gaskiya a game da cutar Ebola na zama babban nakasu ga yaki da cutar a yammacin Afrika.

Kawo karshen annobar Ebola a yammacin Afrika abu ne da zai bukaci a kalla a samar da cibiyar da za ta dauke kashi saba'in cikin dari na marasa lafiya da suka harbu da kwayoyin wannan cuta a cewar cibiyar da ke lura da kaucewa bazuwar cutittika ta Amurka CDC.

Ayyukan lura da wannan cuta ta Ebola karkashin cibiyar da ke lura da ayyukan kula da lafiyar jama'a ta Amurka ya nunar da cewa idan har ba a samu karin kayan agaji ba kuma mutane ba su sauya halayyarsu ba misali binne mamatan ba ta hanyar da ta dace ba cutar za ta iya kama kama mutane 550,000 a Laberiya da Saliyo.

Har ila yau cibiyar ta CDC ta ce annobar na iya shafar wajen mutane milyan daya da dubu dari hudu cikin watanni hudu da ke tafe, kasancewar ba a bada bayanai sahihai yadda ya kamata kan bazuwar cutar a kasashen na yammacin Afrika.

Wannan rahoto na zuwa ne a dai dai lokacin da shugabar kasar Saliyo ke cewa ma'aikatan jinya sun gano gawarwaki da marasa lafiya da dama adaidai lokacin da suka gudanar da kwanaki uku na kullen jama'a a wani bangaren yunkurin gwamnatin kasar na yaki da bazuwar cutar ta Ebola.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Suleiman Babayo