Ebola-mutuwa ta biyu a kasar Mali
November 12, 2014Talla
Wannan dai shine ya kawo adadin wadanda suka mutu sakamakon cutar ta Ebola a kasar Mali zuwa mutane biyu, bayan da wata yarinya mai kimanin shekaru biyu da kakarta ta dauko ta ita ma da ga Gini ta ce ga garinku nan sakamakon cutar ta Ebola. Sai dai rahotanni sun nunar da cewa mutuwar jami'ar jinyar ba ta da nasaba da mutuwar yarinyar 'yar shekaru biyu, wadda ta mutu a kasar cikin watan Oktoban da ya gabata.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu