Duniya ta yi kira a kai hankali nesa a Burundi | Siyasa | DW | 14.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Duniya ta yi kira a kai hankali nesa a Burundi

Sakamakaon tsananta da rikici ke yi a Burundi, kasashen duniya sun nuna rashin amincewarsu da yunkurin juyin mulki. Ita kuwa MDD ta shirya wani taro da ke maida hankali kan halin da ake ciki a kasar.

Kungiyar kasashen gabashin Afirka wadda Burundin ke cikin jerin mambobinta ta ce za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin kasar ta koma kan tafarkin dimokaradiyya kamar kowacce kasa ta yankin. Shugaban Tanzaniya Jakaya kikwete da ya yi magana da yawun shugabannin yankin ya ce suna ganin abin da ya faru a kasar Burundi ba zai taba warware rikicin siyasar kasar ba.

Kikwete ya ce "kungiyarmu na da ra'ayin cewar juyin mulki ba zai kawo karshen sa toka sa katsin da ake fuskanta a fagen siyasar Burundi ba. Muna sake jaddadawa duniya cewar ba mu amince da juyin mulkin ba kuma muna Allah wadai da shi. Muna son ganin an maida harkokin dimokaradiyya a kasar kuma za mu ci-gaba da sa idon don ganin lamura sun daidaita a kasar."

Burundi Präsident Pierre Nkurunziza

Nkurunziza ya ce har yanzu shi ne shugaban Burundi

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban-ki Moon ya ce suma kamar kungiyar ta kasashen gabashin Afirka suna sanya idanu kan lamuran da ke wakana a kasar kana Majalisar na tunasar da 'yan Burundi bukatar da ake da ita wajen samun zaman lafiya.

Stephene Dujarric shi ne ya ke magana da yawun Sakatare Janar din na Majalisar Dinkin Duniya. Ya ce "muna sanya idanu kan lamuran da ke wakana a kasar, muna kuma magana daga lokaci zuwa lokaci da manzonmu na musamman kan kasar ta Burundi wanda yanzu haka ya ke Tanzaniya. Sakatare Janar na tunasar da shugabannin Burundi din bukatar da ake da ita ta samun zaman lafiya a kasar wadda a baya ta sha fama da tashin hankali."

Masharhanta irinsu Yolande Bouka na ganin sukar da ake yi ga soji kan juyin mulki da kiran maido da tsarin dimokaradiyya musamman ma daga shugabannin yankin tamkar ungulu da kan zabo ne domin kuwa Burundin na kewaye ne da kasashen da shugabanninsu suka yi shuhura wajen yin karar tsaye ga dimokaradiyya din.

Militärputsch in Burundi

fargaba ta sa mazauna Bujumbura zama a gidajensu

Ta ce "duk da cewar shugabannin gabashin Afirka da ke kan gaba wajen la'antar juyin mulkin Burundi, akwai fa a cikin shugabannin da ke da hallayya iri daya da Shugaba Nkurunziza. Burundi na kewaye fa da kasashen da shugabanninta ke da ra'ayin watsi da wa'adin mulki da kundin tsarin mulkin kasashensu ya gindaya.

Yanzu haka dai al'umma a sassa daban-daban na duniya na ci-gaba da zuba idanu don ganin irin alkiblar da kasar ta Burundi za ta fuskanta a daidai wannan lokaci da ta ke tsaka da rikici na siyasa.

Sauti da bidiyo akan labarin