Duniya ta kunshi nau′in itatuwa sama da dubu 60 | Labarai | DW | 05.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Duniya ta kunshi nau'in itatuwa sama da dubu 60

Sakamakon wani rahoton bincike da wata kungiya mai fafutukar kare itatuwa a duniya ta wallafa kan nau'o'in itatuwa a duniya, ya nunar da cewa ya zuwa yanzu duniya na kunshe da nau'in itatuwa dubu 60 da 65. 

Sakamakon wani rahoton bincike da wata kungiya mai fafutukar kare tsirrai da itatuwa a duniya ta wallafa a wannan Laraba kan nau'o'n itatuwa da ke da akwai a duniya, ya nunar da cewa ya zuwa yanzu duniya na kunshe da nau'in itatuwa dubu 60 da 65. 

Rahoton kungiyar ta BGCI wato Botanic Garden Conservation International, da ke da cibiyarta a birnin London ya nunar da cewa kasar Brazil ce ke a sahun gaba da nau'o'in itatuwa 8,715 Kwalambiya na bi mata da nau'in itatuwa 5,776 kana Indunusiya na a matsayin ta uku da nau'i 5,142.  

Sai dai rahoton ya ce daga cikin adadin nau'o'in itatuwar da aka yi rijista akwai kimanin 9,600 da ke fuskantar barazanar bacewa daga doron kasa, musamman a sakamakon ayyukan saran dazuka. Wannan aiki na kidayar nau'o'in itatuwan na da burin kare wadanda ke fuskantar barazanar bacewa daga doron kasa.