1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a rage amfani ta leda a duniya

Abdullahi Tanko Bala
March 15, 2019

Kasashe mambobi a Majalisar Dinkin Duniya sun amince a wannan Juma'ar za su rage yawan amfani da leda da robobi nan da shekaru goma masu zuwa.

https://p.dw.com/p/3F9hn
Nairobi - erste Sitzung der neu eingerichteten Umweltversammlung der Vereinten Nationen UNEA
Hoto: picture-alliance/Landov

Kasashen sun dauki wannan alkawarin ne a babban taron Majalisar Dinkin Duniya kan muhalli da aka kammala a birnin Nairobi na kasar Kenya.

Kasashen sun kuma yi alkawarin daukar matakan magance matsalolin muhalli da suka hada da ledoji da dangoginsu nan da shekarar 2030

Sai dai sanarwar bayan taron ta sassauta bisa bukatar Amirka wadda ta nuna adawa da daukar matakai masu tsauri kan kayayyaki masu gurbata muhalli.

Tun da farko dai an yi fatan cewa kasashen za su haramta amfani da leda baki daya. 

A cewar shugaban zauren Majalisar Dinkin Duniya Siim Kiisler yana da matukar wuya a iya samar da matakin bai daya ga dukkan kasashe.