Duniya na kasaw a yaki da Ebola
October 15, 2014Talla
Duniya na kara nuna kasawa a yaki da cutar Ebola, a cewar wakilin MDD kan cutar Ebola Anthony Banbury. Banbury yace cutar ta riga ta yiwa masu yaki da ita fintinkau, don haka shawo kanta zai dau lokaci. Inda babban jami'in ya ce mai yiwuwa kan nan da karshen shekara a gano karin wasu mutane dayawa dauke da cutar. Banbury da yake magana a zauren MDD kan cutar Ebola, ya kara da cewa yadda cutar ta tserewa masu yaki da ita, ya zama wajibi ko dai a dau matakan gaggawa yanzu, ko kuma duniya ta dandani kuda bisa radadi da kuma illar da cutar za ta haddasa nan gaba.