Duniya na da aiki a gaba a yaki da Ebola. | Labarai | DW | 02.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Duniya na da aiki a gaba a yaki da Ebola.

Masana a harkar lafiya a duniya na bukatar kasashen duniya su yi wa cutar Ebola taron dangi dan murkusheta saboda barazanarta ga rayuwar dan Adam

Kungiyar likitoci ta Nagari na Kowa Medecins sans Frontieres ta kasa da kasa ta bayyana cewa bisa dukkan alamu duniya na neman gazawa a yaki da cutar Ebola kasancewar MDD ta yi gargadin cewa za a iya fiskantar karancin abinci a yankunan da wannan cuta tafi yin barna.

Kungiyar ta MSF ta fadawa MDD a birnin Newyork cewa shugabanni na kasashen duniya na gazawa a yakin da suke yi da wannan annoba, saboda haka sai suka bukaci shugabannin da su tasamma wannan annoba mai kudirin kare dangi na halittun dan Adam a duniya su aika da kayan agaji da maaikatan lafiya zuwa yammacin na Afrika.

Kungiyar likitocin ta ce a cibiyarta ta Laberiya da Saliyo mutane sun yi yawa hakan yasa mutane na mutuwa cikin iyalansu. A Saliyo wasu mutane da suka mutu ta sanadin kwayoyin cutar Ebola na mutuwa gawarsu na rubewa a tituna.

Kididdiga ta baya-bayannan da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta fitar, ta nuna cewa mutane 1,552 suka mutu wasu kuma 3,062 suka harbu da kwayoyin cutar.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita :Usman Shehu Usman