Dubban ′yan Iraki na zanga-zanga a birnin Baghdad | Labarai | DW | 27.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dubban 'yan Iraki na zanga-zanga a birnin Baghdad

Dubban 'yan kasar Iraki ne a yau suka futo kwansu da kwarkwata a kan titunan birnin Baghdad domin gudanar da wata zanga-zanga da nufin tilastawa mahukuntan kasar yin wani garambawul a majalisar zartarwar kasar.

Kasar Iraki dai na fusakantar matsalolin siyasa, a yayin da Firiminisatan kasar Haider al-Abadi ke cigaba da kokarin kafa sabuwar majalisar zartarwar kasar da zata hado dukkanin bangarorin da basa ga miciji da juna.

Masu zanga-zangar dai na son ganin Shugaba Haider al-Abadi daukar kwararan matakan yin tankade da rairaya a cikin gwamnatin gami da kawo karshen cin hancin da rashawar da ya yiwa kasar katutu.

Bugu da kari a yayin da duban 'yan Irakin ke cigaba da zanga zangar, tuni 'yan majalisar dokokin Irakin suka amince da nada karin wasu da Shugaba Haider al-Abadin ya mika musu wadanda za a dana a mukaman ministocin kasar.