Dubban jama′a na yin ƙaura daga Ukraine | Labarai | DW | 25.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dubban jama'a na yin ƙaura daga Ukraine

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce sama da mutane dubu 230 tashin hankalin da ake yi a Ukraine ya tilastawa ficewa daga gidajensu.

A cikin wani rahoton da hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar ta Ɗinikin Duniya ta bayyana a yau, ta ce kimanin mutane dubu ɗari suka canza wurin zama a yankin gabashi da na kudancin ƙasar na Ukraine.

Addadin da ta ce ya ninka a cikin wata guda, yayin da wasu dubu 130 suka ƙwamace tserewa zuwa Rasha. Yazuwa yanzu mutane kusan dubu suka rasa rayukansu a faɗan da ake yi tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan aware.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu