1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Donald Tusk zai ci gaba da jagoranci a EU

Abdul-raheem Hassan
March 9, 2017

Shugabannin kasashen Turai sun sake zaben Donald Tusk a matsayin shugaban hukumar hadin kan Tarayyar Turai, wannan dai shi ne karo na biyu da dan asalin kasar Poland zai ja ragamar wannan hukuma.

https://p.dw.com/p/2YvQW
Großbritannien EU-Ratspräsident Donald Tusk
Shugaban majalisar Tarayyar Turai, Donald TuskHoto: picture-alliance/dpa/A. Rain

A yayin wani taron koli da ya gudana a wannan Alhamis a birnin Brussels na kasar Beljiyam, shugabannin kasashen Turai 27 ne suka zabi Tusk dan asalin kasar Poland domin ya sake jagorantar hukumar hadin kan Turai na tsawon shekaru biyu da rabi.

To sai dai wannan zabe na Tusk, na ci gaba da shan suka daga wakilan kasarsa ta haihuwa wato Poland. Amma shugaban ya wallafa a shafinsa na twitter jim kadan bayan zabensa cewar zai iya bakin kokarinsa na ganin ya inganta Tarayyar kasahen Turai.