1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Donald Trump ya gargadi Cuba a kan dukiyar Venezuela

January 11, 2026

Amurka ta gargadi kasar Cuba dangane da dogaro da arzikin kasar Venezuela tsawon lokaci. Shugaba Trump ya ce kasar ba za ta sake samun wani kudi ko albarkatun man Venezuela ba.

https://p.dw.com/p/56eN0
Hoto: Pablo Porciuncula/Saul Loeb/AFP

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi wa Cuba gargadin da ta nemi wata yarjejeniya da Amurka, ko kuma ta fuskanci abin da ya kira mummunan sakamako.

Mr. Trump ya ce daga yanzu Cuba ba za ta kara samun kudi da man fetur daga kasar Venezuela ba.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Truth Social, Trump ya ce yana karfafa wa Cuba gwiwa don ta saurara tun da wuri kafin lokaci ya kure mata.

Wannan bayani na Donald Trump ya zo ne mako guda bayan da sojojin Amurka suka kama shugaban Venezuela, Nicolás Maduro.

Shugaba Trump ya kuma yi isharar cewa sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, na iya zama shugaban Cuba a nan gaba.

kasar Cuba dai ta dade tana cin gajiyar man fetur daga Venezuela bisa yarjejeniyoyin da aka kulla tsakanin kasashen biyu a zamanin tsohon shugaban Caracas, Hugo Chávez.