Dokar yaki da ta′addanci ta fara aiki a Masar a wani yunkurin fatattakar ′yan tarzoma | Labarai | DW | 17.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dokar yaki da ta'addanci ta fara aiki a Masar a wani yunkurin fatattakar 'yan tarzoma

Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi ya amince da sabuwar dokar yaki da ta'addanci da ta danganci yada labarai da kuma kariya ga jami'an tsaron kasar.

Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi

Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi

A karkashin wannan sabuwar doka dai duk wanda ya yada labaran karya dangane da abin da ya shafi yaki da tsageru ko kuma hare-hare daga tsagerun zai biya tara kana ta tanadi kafa wasu kotuna na musamman da kuma kariya ga dakarun sojoji da jami'an 'yan sandan kasar. Tuni dai dokar ta fara fuskantar suka, inda 'yan adawa ke mata kallon ta kokarin murkushe 'yancin kafafen yada labaran kasar tare kuma da nuna fargabar cewa sabuwar dokar ka iya hana 'yan jaridu bayar da rahotanni dangane da yakin da ake yi da tsagerun cikin 'yanci. Hare-haren da Masar ke fuskanta daga tsagerun gundumar Sinai ta kasar a 'yan kwanakin nan dai sun hallaka daruruwan sojoji da 'yan sandan kasar. Kisan da aka yi wa babban mai shigar da kara na gwamnatin Masar a karshen watan Yunin da ya gabata na daya daga cikin abin da ya sanya gwamnatin kasar yin azama tare da gaggauta amincewa a sabuwar dokar ta yaki da ta'addanci.