Dokar tatsar bayanan sirri ta Amirka | Labarai | DW | 01.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dokar tatsar bayanan sirri ta Amirka

Majalisar dattawan Amirka ta gaza amincewa da kara wa'adin dokar tatsar bayanan sirrin jama'a a asirce mai taken Patriot Act.

Dokar ta Patriot Act da ke bayar da dama wajen nadar bayanan sirrin jama'a a wayar salula da ke zaman daya daga cikin dokokin yaki da ta'addanci na kasar na karewa. A wani takaitaccen zama da majalisar dattijai ta yi a wannan Lahadi da ta gabata ta ki kara wa'adin dokar da ke bai wa hukumar tsaron Amirka damar tatsar bayanan al'ummar kasar na wayar tarho a asirce. Da yake mayar da martani bisa wannan batu, Shugaba Barack Obama na Amirkan cewa ya yi:

"Ba za mu sarayar da dokar da ke taimaka mana wajen kare kanmu ba. Zai zama sakaci da rashin sanin madafa. Ba za mu bar hakan ya faru ba."

Fadar mulkin Amirka ta White House dai na kokarin mika wa majalisar dokokin kasar wata doka da za ta maye gurbin dokar ta tatsar bayanai, wadda za ta baiwa hukumar tsaron kasa damar sauraran wayoyin tarhon da aka yi a Amirka. Sai dai tuni ita ma wannan dokar ta fara samun suka daga 'yan adawa irin su Rand Paul dan takarar shugabancin kasar karkashin babbar jam'iyyar adawa ta Republican.