Dokar hana yawo, farin cikin matan Borno | Zamantakewa | DW | 16.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Dokar hana yawo, farin cikin matan Borno

Matan aure a Maiduguri na jihar Borno a Najeriya, sun yaba da matakin takaita zirga-zirgar jama'a daga karfe 8:00 na yamma zuwa wayewar gari suna mai bukatar wasu ranaku a mako da wannan doka za ta ci gaba da aiki.

Mata a birnin Maiduguri a jihar Borno, Najeriya

Mata a birnin Maiduguri a jihar Borno, Najeriya

A farkon watan nan na Janairu ne dai gwamnatin jihar ta Borno ta sanar da tsawaita dokar hana zirga-zirga a Maiduguri babban birnin jihar inda aka maida lokacin shiga zuwa karfe 8 na yammaci maimakon karfe 10 da dare inda za iya fara fita daga daga karfe 6 na safiya. Dokar wacce ta wucin gadi ce, ta faranta wa da dama daga matan aure a Maidugurin saboda yadda mazajensu ke komawa gida da wuri sabanin da, da sai cikin dare mazajen nasu ke komawa gare su.

A cewar yawancin matan auren hakan na bada damar zama na tsawon lokaci a gida kuma yana haifar da fahimtar juna tsakanin iyalai da dama. Haka kuma akwai yara da suke samun hira da iyayensu maza ganin yawanci kafin iyayen su dawo yaran sun yi barci. A cewar Esther Jerry, su dai ba abin da za su ce sai sam barka da matakin. 

Sai dai mazajen a nasu bangaren, suna kokawa da yadda dokar ta shafi sana'o'in su. Malam Bukar na unguwar Bolori a Maiduguri, ya ce wannan mataki ya haifar musu da takura gami da koma baya  a harkokin neman abin da za su ciyar da iyalansu musamman ganin akwai kasuwannin da sai da dare su ke ci.

Wata 'yar Borno a zaune cikin zulumi

Wata 'yar Borno a zaune cikin zulumi

Wasu ma da ba su ji dadin wannan doka ba, su ne 'yan mata da ke neman mazajen aure wadanda suka ce hira ta waya da samari ba za ta gamsar da masu neman aure ba, sai dole ana hira irin wacce al'adun yankin su ka amince da ita. Masana zamantakewa, sun yi imanin cewa wannan mataki ya haifar da ingantuwar dangantaka da fahimtar juna tsakanin ma‘aurata kuma aurarraki da dama sun gyaru.