Dokar bindiga a Florida | Labarai | DW | 08.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dokar bindiga a Florida

Hukumomi a jihar Florida da ke kasar Amirka sun amince da dokar mallakar bindigogi sakamakon wata asarar da aka tabka sanadin hari da wani ya kai wata makaranta.

Majalisar dokokin jihar Florida a Amirka, ta amince da sabuwar dokar mallakar makamai, makonni da halaka mutum 17 da wani dan bindiga ya yi a wata makaranta a jihar. Dama dai kudurin dokar ya bukaci kara shekarun iya mallakar bindiga ne zuwa 21 daga 18 na yanzu, da kuma bai wa jami'an 'yan sanda karfin kwace makami. Haka nan ma akwai batun bullo da wani shiri da zai rika samar da makamai ga wasu malaman makarantu.

Wakilai 67 ne dai suka amince da dokar, yayin da wasu 50 din suka bijire, sai dai duk da hakan sai dokar ta sami sahalewar gwamnan jihar Rick Scott, kafin ta kai ga kama aiki. Shi dai gwamna Scott ya ce zai gana da iyalan wadanda aka kashe wa 'ya'ya a harin na makaranta, kafin ya rattaba hannu.