Dilma ta fara wa′adin mulkinta na biyu | Labarai | DW | 02.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dilma ta fara wa'adin mulkinta na biyu

Shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff ta yi alkawarin tsuke bakin aljuhu domin ta inganta halin rayuwar talakawa a wa'adin mulkinta na biyu dake farawa.

Shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff ta fara wa'adin mulkin na biyu watanni kusan uku bayan samun damar yin tazarce da ta yi a zaben da ya gudana a watan Oktaba na shekarar da ta gabata. Shugabannin kasashen da dama ciki har da Latin Amirka da na China da kuma mataimakin shugaban kasar Amirka ne suka halarci bikin rantsar da ita a Braziliya babban birnin wannan kasa.

Dilma Rousseff mai shekaru 67 a duniya ta yi alkawarin inganta halin rayuwan talakawan Brazil tare kwadaitawa 'yan kasuwa zuwa zuba jari a kasar domin tattalin arzikinta ya bunkasa. Ta ce za ta sa kafar wando guda da cin hantsi da karbar rashawa, tare da samar wa matasan aiki yi. sannan ta nunar da cewa za ta rage yawan kudin da gwamnati ta swaba kashewa a kowace shekara.

A wa'adin mulkinta na farko shugabar ta Brazil ta fuskanci kalubale a fannin tattalin arziki sakamakon koma bayan da ta addabin manyan kasashe na duniya. Kana gwamnatinta ta yi kaurin suna a fusakar cin hanci da karbar rashawa musamman ma a fannin cinikin man fetur a kanfanin Petrobas.