1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnan Florida zai kalubalanci Trump a Amirka

May 25, 2023

Dan siyasar mai shekaru 44 da ake siffantawa a matsayin matashi a cikin masu zawarcin kujerar shugaban Amirka shi ne ake ganin ka iya kawo wa tsohon shugaban Amirka Donald Trump komabaya a jam'iyyar Republican.

https://p.dw.com/p/4RnBc
Hoto: Paul Hennessy/SOPA Images via ZUMA Press Wire/picture alliance

Bayan watannin da aka kwashe ana rade-radi, gwamnan jihar Florida ta Amirka  Ron DeSantis ya sanar da aniyarsa ta neman takarar shugaban kasa. DeSantis ya sanar da haka ne a wani sakon murya a shafinsa na Twitter wanda ya fuskanci tangardar na'ura a yayin da yake aike wa da sakon kai tsaye sakamakon abin da mahukuntan Twitter suka ce yawan masu kallo da sauraro ne ya janyo hakan.

Babban burinsa dai shi ne dawo da martabar Amirka ta hanyar gina katanga a tsakanin Amirka da Mexico domin abin da ya kira kama masu safarar miyagun kwayoyi.

Sauran 'yan takarar da ke neman Republican din ta tsayar da su takara sun hada Sanata Tim Scott da tsohuwar wakiliyar Amirka a MDD Nikki Haley.