1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Deby ya yi bazaranar janye sojojinsa a Afirka

Salissou Boukari
June 26, 2017

Shugaban kasar Chadi Idriss Deby Itno ya yi barazanar janye dukannin sojojin kasarsa da ke ayyukan tsaro a wasu kasashen Afirka, muddin ba a dauki matakin kawo wa kasarsa tallafin kudi ba.

https://p.dw.com/p/2fMcF
Tschadische Soldaten bei Rückkehr aus Mali 13.05.2013 mit Präsident Idriss Deby Itno
Shugaban Chadi idriss Deby tare da sojojinsaHoto: STR/AFP/Getty Images

Yayin wata hira ce da aka yi da shi ta kafofin yada labaran kasar Faransa, Shugaba Deby ya ce ko kadan ba su samu wani tallafi na kudi ba a famar da suke da tarin matsaloli na tattalin arziki da kuma boren al'umma. Kuma idan aka ci gaba da hakan zai zame musu dole su janye sojojin da suke da su a wasu kasashen nahiyar.

A kasar Mali, kasar Chadi ce ta uku wajen samar da sojoji mafi yawa a rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta MINUSMA, inda take da sojoji 1.390, sannan kuma wasu sojojin na Chadi 2000 na cikin rundunar kawance ta Najeriya, Nijar, Chadi da kuma Kamaru masu yakar 'yan Boko Haram, inda ya ce hakan mataki ne da ke da tsadar gaske a garesu.