Dawo da kafofin sada zumunta a Chadi | Labarai | DW | 13.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dawo da kafofin sada zumunta a Chadi

Shugaba Idriss Deby na kasar Chadi ya bayar da umarnin dage haramcin amfani da kafofin sadarwa na zamani da aka yi a kasar.

Shugaban da ke jawabi a gaban taron kamfanonin sadarwar zamani, ya ce an dauki matakin ne bisa dalilai masu nasaba da barazanar tsaro a sakamakon aikin ta'addanci.

Inda ya umarci kamfanonin, da su mayar da hanyoyin sadarwar. Wani dan jaridar kafar yada labaran Faransa na AFP,  ya ce jama'a sun sami damar amfani da internet a wannan Asabar, musanman ma'abota hanyoyin aika sakonnin na watsapp da kuma Twitter.

Kasar Chadi da ke samun goyon bayan kasashen yamma a yakin da ta ke da ayyukan mayakan jihadi, ta kasance kasar da ke fuskantar barazana daga kungiyar Boko Haram, da sau da dama ke kai mata hare-hare ba kaukautawa. A watan Maris bara ne Shugaba Idriss Derby ya bayar da umarnin toshe hanyoyyin sada zumunta da ake ganin na taimaka wa 'yan ta'adda gudanar da ayyukansu.