Daura danbar yaki da cin hanci a Ukraine | Labarai | DW | 14.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Daura danbar yaki da cin hanci a Ukraine

Sabon Firaministan Ukraine Volodymyr Groysman ya lashi takobin yaki da ci hanci da rashawa.

Da gagarumin rinjaye majalisar dokokin kasar Ukraine ta zabi kakakin majalisa kuma mai ra'ayin kasashen yamma, Volodymyr Groysman a mukamin sabon Firaministan kasar. A jawabinsa ga wakilan majalisar Groysman ya lashi takobin yaki da cin hanci da rashawa, kana ya ce zai gaggauta aiwatar da canje-canje bisa wannan manufa. Ya ce dole ne aikin da gwamnati ke yi ya zama mai cike da gaskiya da adalci. Bayan kwanaki da dama na tattaunawa, a ranar Laraba kawancen da ke goyon bayan kasashen yamma ya share hanyar kafa sabuwar gwamnati. Groysman dan shekaru 38 da haihuwa, shi ne dai dan takarar da ya fi samun goyon bayan shugaban kasa Petro Poroshenko, shi ne kuma Firaministan Ukraine mafi karancin shekaru a tarihin kasar. A ranar Lahadi Firaminista mai barin gado Arseniy Yatsenyuk ya yi murabus bayan gwamnatinsa ta shafe watanni tana fama da rikici.