Daniel Galvan ya shiga hannun mahukuntan Spain | Labarai | DW | 05.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Daniel Galvan ya shiga hannun mahukuntan Spain

Bayan da sarkin Morocco ya janye afuwar da ya yi ma sa, Daniel Galvan ya ficce daga ƙasar ya nufi Spain, to sai dai haƙonsa bai cimma ruwa ba tunda mahukunta sun cafke shi

epa03813863 An undated handout image provided by Casblanca's daily newspaper Al Massae on 05 August 2013 shows Spanish paedophile Daniel Galvan Fina, who was convicted of rape of eleven Moroccan children and sentenced to 30 years in jail in Morocco. A palace statement issued on 04 August 2013 said that King Mohamed VI has revoked his royal pardon to Fina, following protests in Morroco. EPA/AL MASSAE / HANDOUT HANDOUT EDITORIAL USE ONLY/NO SALES

Daniel Galvan Fina

'Yan sanda a ƙasar Spain sun kame mutumin nan mai lalata da ƙananan yara wanda sarkin Morocco, Mohammed na shidda ya janye afuwar da ya yi masa bayan da matakin ya janyo zanga-zanga a ƙasar.

Daniel Galvan mai shekaru 64 na haihuwa wanda kotu ta same shi da laifin yiwa yara 11, 'yan shekaru huɗu zuwa 15 fyaɗe, aka kuma yanke mishi hukuncin ɗauri na shekaru 30 a kurkuku ya shiga hanun jami'an tsaron Spain ne a garin Murcia da ke yankin kudu maso gabashin Spain, bisa bayanan da mai magana da yawun ma'aikatar cikin gidan ƙasar ya bayar

Ministocin shari'an Morocco da Spain sun tattauna wannan batu ta wayar tarho inda suka yi alƙawarin yin hadin kai dan ɗaukar mataki na bai ɗaya dangane da wannan matsala.

To sai dai ana ganin zai yi wahala a ce Spain ta miƙa Daniel Galvan a yi masa shari'a a wata ƙasa ta daban kasancewar bata yadda da miƙa 'yan ƙasarta haka nan.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Usman Shehu Usman