Dan sanda ya rasu a hannun mahukunta a Kaduna | Labarai | DW | 31.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dan sanda ya rasu a hannun mahukunta a Kaduna

Rundunar 'yan sandan ta ce za tacigaba da bincike harsai ta gano duk wadanda suke da hannu cikin wannan badakalar da ta yi sanadiyyar salwantar ran wannan dan sanda.

Suleiman Abba, Generalinspektor der nigerianischen Polizei

Suleiman Abba, Sfeto Janar na 'yan sandan Najeriya

Rundunar 'yan sandan jahar kaduna ta bayar da tabbacin rasuwar wani jami'inta da ta kama shi da hannu dumu-dumu wajan safarar wasu bindigogi da makaman da za a kai wasu jihohi da ke da makwapta da Kaduna Rundunar 'yan sandan ta gudanar da wani taran manema labarai na gaggawa da yammacin nan, inda ta bayyana mutuwar wannan dan sanda da ta tsare domin samun damar gudanarda bincike, kafin ya gamu da ajalinsa

S.P Aminu Lawal shi ne kakakin rundunar 'yan sandan, wanda kuma ya jagoranci wannan taran manema labarai, ya nunar da cewa za su ci-gaba da gudanar da wannan bincike da sauran mutane biyun da aka kama sun zo sayen bindigogin