1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Dan hamayya na kan gaba a zaben Senegal

March 25, 2024

Bayanan da ke fara fitowa daga Senegal, na nuna dan takara a zaben shugaban kasar, Bassirou Diomaye Faye na kan gaba a wannan safiya ta Litinin.

https://p.dw.com/p/4e58A
Dan hamayya a zaben Senegal, Bassirou Diomaye Faye
Hoto: SEYLLOU/AFP

Sakamako da aka tattara kawo i yanzu na nuna dan takarar na hamayya Bassirou Diomaye Faye na iya kai labari a zaben da ya biyo bayan shekaru da dama na rigingimun siyasa a Senegal.

To amma kuma bangaren hadaka a jiya Lahadi na cewa ba makawa za a je zagaye na biyu.

A fili yake dai Bassirou Diomaye na gaban dan takarar hadaka ta gwamnatin Senegal din kuma tsohon firaminista Amadou Ba

Duk dan takarar da lashe zaben na Senegal dai, na iya zama mutumin da ake yi wa fatan fitar da kasar daga kangin da take ciki.

Haka ma ana ganin shi ne wanda zai gudanar da makudan kudaden da kasar za ta samu daga albarkatun mai da iskar gas jim kadan bayan fara hakowa.

Tuni ma mace daya tilo a zaben, Anta Babacar Ngom, ta taya dan takar na hamayya murna a shafinta na X da aka sani da Tuwita a baya.