1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dan bingiga ya kashe mutane a Amirka

November 20, 2018

Wani dan bindiga ya bude wuta a wani asibitin birnin Chicago na kasar Amirka, inda ya halaka mutum uku ciki har da wani likita da kuma jami'in dan sanda.

https://p.dw.com/p/38Yd9
USA Chicago Prozess gegen den Polizisten Jason Van Dyke | Tatwaffe
Hoto: Reuters/Chicago Tribune/A. Perez

Magajin garin birnin na Chicago da kuma ofishin hukumar 'yan sanda, sun ce daya daga cikin wadanta suka mutun wata mata ce da ke aiki a asibitin na Mercy Hospital da abin ya faru.

Shi ma dan bindigar ya mutu, sai dai ba a tabbatar da ko ya mutu ne sakamakon musayar wutar da suka yi da jami'an 'yan sanda ko kuma kashe kanshi ya yi da kanshi ba. Shi dai dan bindigar sai da ya auni wajen da mutane ke masu yawa kafin ya buda wutar.

Lamarin kuwa kamar yadda bayanai ke nunawa ya samo asali ne daga wata 'yar hatsaniya da ta kaure a wajen ajiye motoci na asibitin.