Dan bindiga ya bude wuta a Turkiyya
January 1, 2017Talla
Ministan cikin gida na Turkiyya ya ce daga cikin wadanda suka mutu har da 'yan kasashen waje guda 19. Wanda ya kai harin ya yi shigar burtu a gidan rawar sannan ya bude wuta a kan jama'ar daf da lokacin ake yin bukukuwan shiga sabuwar shekara ta 2017. Hukumomi a kasar dai sun ce suna ta kokari wajen damke wadanda ke da hannu wajen shirya wannan hari yayin da a share guda kasashen duniya ke cigaba da aikewa da sakonninsu na jaje ga mahukuntan Turkiyya din.