Damuwar al′umma bayan harin da aka kai Gombe a Najeriya | Siyasa | DW | 23.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Damuwar al'umma bayan harin da aka kai Gombe a Najeriya

Bayan jana'izar wandanda suka rasu a hare-haren da aka kai a wasu tashoshin mota a Gombe, jama’a na ta tururuwa zuwa asibitoci domin duba ‘yan uwa da abokan arziki.

An dai gudanar da jana’izar ce kashi-kashi, inda jama’a da dama suka halarta don yin addu’o'i ga wadanda suka riga mu gidan gaskiya tare da fatan Allah ya kawo karshen wannan matsalar. Kusan duk wuraren da jama ke zama a cikin garin musamman wuraren da al’amarin ya auku an samu takaitar harkoki, inda aka rufe tashoshi da aka tada bama-bama tare da tsananta sa ido don magance yin satar kayan jama’a da ke cikin shaguna a rufe, sannan kuma daga fuskokin mutane za ka iya gane halin da suke ciki na dimuwa da fargaba, tare da nuna alhinin abun da ya faru wanda ke zama na biyu a cikin kwanaki shida bayan wanda aka kai a babbar kasuwar Gombe inda jama’a da dama suka mutu.

Ana jiran fitowar sakamakon adadin karshe

Ya zuwa yanzu dai hukumomi ko jami’an tsaro ba su kai ga fitar da yawan alkaluma na wadanda abin ya rutsa da su ba, inda kakakin rundunar ‘yan sanda ta jiha Fwaje Attajiri ya ce suna ci gaba da tattara bayanai kuma nan gaba kadan za su fitar da sakamakon abinda suka samu. Jama’ar gari kuma na ci gaba da daukar matakai na kare kai, inda ake tsananta binciken masu shiga da fita a wuraren taruwar jama’a musamman wuraren ibada da kasuwanni.

Kira ga gwamnati da ta dauki matakan tsare kasuwanni

To amma wasu ‘yan kasuwar garin Gombe na neman gwamnati ta katange wannan kasuwa domin bada damar yin binciken masu shiga kasuwar ta haka ne a cewar su za’a iya rage irin wadan hare-hare a cikin kasuwanni. Tuni dai Mataimakin gwamnan jihar Gombe Mr Charles Iliya ya ziyarci wuraren da ala’amarin ya auku wanda ya bayyana sakon Gwamnan na jaje da alhinin abinda ya faru tare da yin addu’a ta neman Allah ya kawo karshen matsalar tsaro a kasar ta Najeriya.

Sauti da bidiyo akan labarin