1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

G5 Sahel: Janye sojan Faransa na iya zama illa ga yankin

Abdoulaye Mamane Amadou
December 3, 2020

Babban Commandan rundunar tsaro ta G5 Sahel ya nuna damuwa kan yiwuwar janye adadin dakarun Faransa da ke yaki da ta'addanci a yankin Sahel.

https://p.dw.com/p/3mB8H
Burkinafaso Tofalaga Operation Barkhane
Hoto: picture-alliance/dpa/P. De Poulpiquet

Janar Oumarou Namata Gazama ya ce duba da yadda yanzu hakan rundunonin kasashen Afirka da na faransa  ke aiki kafada da kafada a yankin, batun ragowar sojojin Faransa na Barkhane ka iya haddasa illa ga yakin da dakarun G5 din suke da 'yan ta'adda.

Har yanzu rudunar G5 mai sojojin karo-karo 5 000 daga kasashen Burkina Faso da Mali da Chadi da Murtaniya da Jamhuriyar Nijar, na fuskantar wasu tarin matsalolin kakkabe 'yan ta'addan da suka yi kaka gida a yankin, lamarin da ke tilasta wa rundunar dogaro da mayakan ketare irin su Barkhane da na sojan Amirka wajen zartar da ayyukansu.