1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dambarwar siyasar Nijar na kara zafi

April 23, 2018

Tun bayan da kotun birnin Yamai ta garkame jagororin kungiyoyin fararen hula a gidajan kaso daban-daban, da ci gaba da hana zanga-zanga da gwamnati ke yi, ake ta zargin gwamnatin da kokarin wuce makadi da rawa.

https://p.dw.com/p/2wWfU
Niger Niamey Studentenproteste
Masu fafutika a Jamhuriyar NijarHoto: DW/Abdoulaye Mamane Amadou

Duk da rungumar kaddara da kungiyoyin farar hula suka yi da hana su gudanar da zanga-zanga a Lahadin da ta gabata a Nijar, hukumomi a kasar ta kara daukar tsauraran matakai, inda ta baza jami’an tsaro a muhimman wurare a Yamai babban birnin Nijar din. Matakin da ya hada da sanya jami’an na tsaro har ma a wasu cibiyoyi, ya kuma shafi har da ofishin Moussa Tchangari, daya daga cikin jagororin kungiyoyin fafutuka da a yanzu ke tsare. Rigingimun da suka hada da na dalibai da kuma na fafutikar adawa da dokar kasasfin kudi da kungiyoyin ke cewa dora wa talaka wahala ne ta tsadar rayuwa, idan aka yi la’kari da halin matsin rayuwa da ake ciki.

Niger Polizei in Niamey
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Gwamnatin dai ta ce ta hana zanga-zangar ranar Lahadin ta yi shi ne saboda tashin hankali da dalibai suka yi cikin makon da ya gabata, abin kuma da kungiyoyin ke cewa babu abin da ya hada abin da suka sanya gaba da hujjar da hukumomin suka bayar, yayin da ita kuwa jam’iyyar PNDS tarayya da ke jagorantar kawancen jam’iyyun da ke mulki ta kalubalanci bangaren adawa, tare da dora mata alhakin yin zagon kasa ga harkokin karatu a kasar.

Masu fashin baki dai na dora laifi ne kann mahukuntan Nijar kann abin da suka kira nuna halin ko oho ga batutuwa da ma muhimman matsalolin da suka shafi ci gaban kasa.

Talakawan Jamhuriyar ta Nijar dai sun zura ido don ganin abin da zai wakana a kasar, bayan dakatar da zanga-zangar kungiyoyin da ma halin da karatu ya shiga cikin kwanakin da suka gabata, dai dai lokacin da al’uma ke matukar bukatar ganin sahihan ayyuka a kasa.