1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Damar karshe ga Birtaniya a shirin Brexit

Yusuf Bala Nayaya
March 12, 2019

Jean-Claude Junker da ke shugabantar Hukumar Tarayyar Turai ya bayyana cewa 'yan majalisar Birtaniya na da dama ta amincewa da yarjejeniya ko fatali da ita.

https://p.dw.com/p/3EplF
Frankreich Brexit l Theresa May trifft sich mit Juncker in Strassburg
Hoto: picture alliance/AP Photo/V. Kessler

Shugaban Hukumar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker ya bayyana cewa dukkanin bangarorin biyu na Kungiyar EU da Birtaniya na goyon bayan sake nazartar hanyoyi da za su kai ga warware kulli da ke tarnaki ga shirin fitar Birtaniya daga kungiyar ta EU. Kullin da ke zama kokari na kauce wa sarkakiya kan batun iyakar Ireland ta Arewa.

Juncker da ke shugabantar hukumar ta Tarayyar Turai ya bayyana yammacin Litinin bayan ganawa da Firaminista Theresa May cewa 'yan majalisa a Birtaniya na da zabi da ke zama mai muhimmanci na ko su amince da yarjejeniya da aka gabatar ko kuma su yi fatali da ita.

'Yan majalisar dai ta Birtaniya sun yi watsi da shirin yarjejeniya fita daga Kungiyar Tarayyar Turai da Theresa May ta gabatar masu a watan Janairu. May dai na son Kungiyar EU ta amince da kwaskwarima ga shirin a wannan karo ta yadda za ta iya jan hankali na 'yan majalisa su amince da shirin nata. Junker dai ya ce shirin da ta gabatar na yanzu na zama mafi kyau sai dai ta kwan da sanin babu sauran  wata dama a gaba bayan wannan .