Dakile tsageru masu amfani da kafofin zamani | BATUTUWA | DW | 06.11.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Dakile tsageru masu amfani da kafofin zamani

Faransa za ta yi aiki da wasu kasashen yammacin Afirka kan shawo kan matsalolin amfani da kafofin zamani wajen aikata laifuka bayan wani harin ta'addanci kan sojojin Mali wanda ya yi sanadiyar mutuwar sojoji fiye da 50.

Kwanaki bayan kaddamar da wani harin ta'addanci kan sojojin kasar Mali wanda ya yi sanadiyar mutuwar sojoji fiye da 50, bangarori da dama na ci gaba da taya hukumomin kasar juyayin abin da ya samu, daga ciki har da ministar tsaron kasar Faransa wacce ta kaddamar da ziyarar aiki a wasu kasashen Sahel, sai dai ziyarar na zuwa ne lokacin da kafafen sada zumunta musamman WhatsApp ke taka rawa inda 'yan ta'adda ke amfani da su wajen yada manufofinsu.

Ziyarar ministar tsaron Faransa Florence Parly  a Mali na zuwa ne a yayin da ake cika kwanaki uku da da ayyana zaman makoki da Shugaban Ibrahim Boubacar Keita ya kaddamar a ranar Litinin sakamakon rashin sojojin kasar fiye da 50 a yayin wani harin ta'addancin da mayakan jihadi suka kai a wani barikin sojan kasar.

Ministar ta kara jaddada matsayin Faransa na yaki da t'addanci, tare da bayyana goyon bayan kasar da daukacin na nahiyar Turai game da batun yaki da ta'addanci a yankin Sahel.

Tuni dai ma'aikatar tsaron kasar ta Faransa ta amabaci kaddamar da wani sabon shiri na kakkabe mayakan jihadin da suka yi kaka-gida daga arewacin Mali kan iyakar kasar da Burkina Faso inji ministar tsaron kasar Faransa a yayin ziyara a Mali.

Kungiyoyin jihadi masu gwagwarmaya da makamai dai sun yiwa kasar Mali da Burkina Faso zobe, inda suke ta kai hare-haren ta'addanci da ke halaka sojo da farar hula, kana kuma kungiyoyin a share daya na amfani da kafafen sada zumunta musamman ma manhajar WhatsAapp wajen yada akidunsu da ma irire-iren hare-haren da sukan kai wurare da dama

Sai dai a hira da DW Julie Owono darakatar zartarwa ta kungiyar Internet Sans Frontières cewa ta yi akwai sakaci mai yawa daga gwamnatocin kasashen musamman na yankin Sahel.

Julie Owono dai ta kara da cewa idan har kungiyoyi masu tsananin kishin addini na amfani da shafukan musamman ma manhajar ta WhatsApp  wajen yada manufofin kamata yayi soma gwamnatocin sun dage da wayar da kan jama'a.

Tuni dai rundunar tsaron Faransa ta bayyana kisan daya daga cikin jagororin kungiyoyin jihadin  nan mai suna Ali Maychou a Mali a yayin wani samame da rundunar tsaron ta gudanar a kasar Mali. Daya daga cikin shugabannin kungiyoyin addini masu tsananin kishin islama da mali take fama da su.

 

Sauti da bidiyo akan labarin