Dakarun Turkiya sun kutsa arewacin Iraki | Labarai | DW | 08.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Turkiya sun kutsa arewacin Iraki

Ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin gwamnatin Turkiya da 'yan awaren Kurdawa

Rahotanni daga kasar Turkiya sun nuna cewa rsojojin kasar sun kutsa cikin arewacin kasar Iraki domin sasakar 'yan awaren Kurdawa. Haka ya na zuwa lokacin da wani harin bam a gabashin kasar ta Turkiya ya hallaka 'yan sanda 12 abin da aka daura alhaki kan 'yan awaren na Kurdawa.

Wannan ke zama hari na biyu cikin mako guda inda na farko ya kai ga mutuwar kimanin sojoji 16. Wata majiyar tsaron kasar ta Turkiya ta ce an hallaka mayakan 'yan aware masu yawa lokacin farmakin dakarun gwamnati.