1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun MDD za su ci gaba da zama a Mali

June 30, 2022

Duk da rashin amincewar da suke fuskanta a Mali, Majalisar Dinkin Duniya ta sabunta wa'adin zaman dakarunta a kasar. Malin dai a yanzu na karashin ikon soji ne.

https://p.dw.com/p/4DRvu
Mali | MINUSMA | Friedenstruppen Ägypten
Hoto: Nicolas Remene/Le Pictorium/IMAGO

Majalisar Dinkin Duniya ta amince da sake tsawaita wa'adin zaman dakarunta da ke aikin kiyaye zaman lafiya a Mali da shekara guda, wani mataki da wasu ke ganin na tattare da hadari.

Wani jami'in diflomasiyya da bai so a bayyana sunansa ba, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, wannan wata caca ce, saboda ganin yiwuwar wasu kasashen Turai su janye dakarunsu cikin dakarun na hadaka.

Mali, kasa da ke cikin jerin kasashe matalauta, ta fuskanci juyin mulki a shekarar 2020 da ma wani da aka yi cikin watan Mayun bara, rikicin kuma da ke da tushe da tsananin rashin tsaro da kasar ke fama da shi.

Sojojin kasar sun juya wa Faransa da ta 'yanta kasar inda a yanzu ta hada kai da Rasha da nufin murkushe mayaka masu ikirarin jihadi da suka addabi kasar.

Akalla sojojin Majalisar Dinkin Duniyar 175 suka mutu a Mali tun bayan kai su cikin rundunar nan ta MINUSMA a 2013.