Dakarun Isra´ila sun kai hari ga gidan kurkukun Jericho na Palestinu | Labarai | DW | 14.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Isra´ila sun kai hari ga gidan kurkukun Jericho na Palestinu

Shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas ya kai ziyara aiki a ƙasar Austriya, inda ya gana da takwaran sa, Chanceler Wolfgang Schüssel, wanda a yanzu, ke riƙe da matsayin shugaban ƙungiyar gamayya turai.

Abbas, yayi anfani da wannan dama, inda ya gayaci shugaba Wolfgang,ya zama kakakin hukumar Palestinawa, wajen sauran ƙasashen EU, na su ci gaba, da bada tallafi ga al´ummomin Palestinu.

ƙungiyar gamaya turai, ta bayana aniyar ta, ta katse hulɗa da hukumar Palestniwa, muddun ƙungiyar Hamas, da zata giraka gwamnati, ba ta yi watsi ba, da aniyar ta, ta yaƙar Isra´ila.

Wannan ziyara na gudana, a yayin da dakarun Isreala, su ka kai hari, a gidan waƙaffin Jericho, dake yankin Palestinu, domin ƙwato wasu mutane,da ta kira yan ta´ada, da su ka haɗa da Ahmad Saadat, shugaban ƙungiyar FPLP, da Israela ke zargi, da hallaka ministan yawan shaƙatawa Rehavam Zeevi.

Mutane 2, su ka rasa rayuka a sakamakon wannan hari da dama kuma sun ji raunuka.

A ɗaya hannun, Palestinawa sun yi garkuwa da yan ƙasashen waje da dama, tare da zargin gwamnatocin su da ɗaurewa Isra´ila gidi.

ƙungiyar haɗin kan larabawa, ta azza alhakin wannan rikici na yau, a kan Jami´an Amurika da na Britania da ke sa iddo ga wannan gidan kurkuku.

A cewar ƙungiyar haɗin kan larabawan, an kai wannan hari, da haɗin kan jami´an ƙasashe 2, da su ka yi ƙasa ko bisa, lokaci kaɗan, kamin harin ya abku.