Dakarun Iraki sun bayyana sake kwato garin Tikrit | Labarai | DW | 28.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Iraki sun bayyana sake kwato garin Tikrit

Gwamnatin Iraki ta kara saka himma wajen kwato yankunan kasar daga hannun masu kaifin kishin addinin Islama

Dakarun sojin Iraki da ke samun rakiyar jiragen saman yaki masu saukan ungulu, sun bayyana sake kwato garin Tikrit, daga hannu tsageru masu kaifin kishin addinin Islama na kungiyar ISIS. Garin na Tikrit da ke zama mahaifar tsohon Shugaban kasar Marigayi Saddam Hussein, na cikin manyan garuruwa na kasar da ya fada a hannun tsagerun.

A daya hannu mayakan 'yan tawayen Siriya da kungiyar Qaeda sun kaddamar da wani harin, domin kwace wani gari na iyaka a Iraki daga hannu tsagerun na ISIL.

Yanzu haka shugabannin jam'iyya mai mulkin kasar ta Iraki na tattaunawa domin samun wanda zai maye gurbin Firamnista Nouri al-Maliki, saboda tunkaran rashin tsaron da kasar ke ciki. Haka ya biyo bayan kiran da manyan malamai shi'a suka yi, na ganin an kafa gwamnati wadda za ta kunshi duk bangarorin kasar, domin kawo karshen rarrabuwa, da samun galaba a yaki da tsageru masu dauke da makamai.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman