Dakarun gwamnatin Somalia sun fatattaki na ´yan Islama daga Bur Hakaba | Labarai | DW | 21.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun gwamnatin Somalia sun fatattaki na ´yan Islama daga Bur Hakaba

Dakarun gwamnatin wucin gadi a Somalia sun fatattaki sojojin sa kai na kawancen ´yan Islama daga wani wuri mai muhimmanci dake birnin Bur Hakaba. Birnin dai na da nisan kilomita 60 kudu maso gabashin birnin Baidoa, mazaunin gwamnatin ta wucin gadi. Ministan yada labaru Ali Jama Jangali ya karyata ikirarin da ´yan Islama su ka yi cewa sojojin Habasha suka marawa sojojin gwamnatin baya. Ita kuma a nata bangaren Habasha ta ce ba ta tura sojojin yaki ba, illa iya ka masu horas da dakaru ta tura don horas da sojojin gwamnatin wucin gadi ta Somalia.