Dakarun Faransa na musamman na wani yakin sirri a Libya inji wani rahoto | Labarai | DW | 24.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Faransa na musamman na wani yakin sirri a Libya inji wani rahoto

Jaridar Le Monde da ta buga wannan labari ta ce Faransa na wani yaki a boye da kungiyar IS mai ikirarin jihadi a Libya.

Jaridar Le Monde ta kasar Faransa ta ce dakarun Faransa na musamman da kwamandojin leken asiri hade da Amirka da Birtaniya na wani yaki cikin sirri da mayakan kungiyar IS a Libya. Jaridar ta ce shugaba Francois Hollande ne ya amince da aikin soji ba bisa doka ba a kasar ta Libya mai gwamnatoci biyu kishiyoyin juna. A wani abin da jaridar ta kira yakin Faransa na sirri a Libya, ta ce dakarun kasar na kai hare-hare kan jagororin kungiyar ta IS, a wani yunkuri na karya karfin kungiyar a Libya. Ma'aikatar tsaron Faransa ba ta ce uffa ga rahoton jaridar ta Le Monde ba, amma majiyoyi na kusa da ministar tsaro Jean-Yves Le Drian sun ce ministan ya ba da umarnin gudanar da bincike kan karya dokokin sirri na tsaron kasar kana kuma a gano inda labarin ya fito.