Dakarun Burtaniya sun janye daga kudancin Afghanistan | Labarai | DW | 17.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Burtaniya sun janye daga kudancin Afghanistan

Dakarun kasar Burtaniya sun janye daga kudancin Afghanistan biyowa bayan bukatar yin hakan da shugabanin kabilun yankin suka yi.

Yankin Musa qala inda dakarun suka janye yana daya daga cikin yankunan da ake samun tashe tashen hankula da hare hare tsakanin dakarun kungiyar tsaro ta NATO da yan kungiyar Taliban.

Kakakin dakarun kungiyar NATO a yankin yace,sun dauki wannan mataki ne bisa bukatun gwamnan lardin.