Dakarun Amirka sun kashe ′yan sanda | Labarai | DW | 22.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Amirka sun kashe 'yan sanda

Rahotannin da ke fitowa daga yankin Kandahar na kasar Afghanistan, na cewa dakarun Amirka sun halaka jami'an 'yan sanda 16, kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar.

Su dai dakarun na Amirka sun kaddamar da lugudan wuta ne ta sama a lardin Helmand, lokacin da jami'an tsaro ke kokarin kakkabe mayakan Taliban a wani kauye da ke lardin. Daga cikin wadanda suka mutun dai har da wasu kwamadodji biyu da kuma wasu da suka ji jiki. Wannan dai wani sabon koma baya ne da ake ganin Amirka ke sake samu, a aikin dawo da kwanciyar hankali a Afghanistan din.

Mai magana da yawun ma'aikatar cikin gidan kasar ta Afghanistan, Najeeb Danish, ya ce suna ci gaba da bincike kan lamarin don taimakawa iyalan wadanda harin ya ritsa da su. Shekaru biyar kenan da sojojin Amirka da Birtaniya ke lardin na Hemland.