Da hannun sojoji a kisan Musulmin Rohingya | Labarai | DW | 10.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Da hannun sojoji a kisan Musulmin Rohingya

A karon farko rundunar sojin kasar Myanmar ta tabbatar da samun wasu jami'anta da hannu a kisan gilla da aka yi wa Musulmin Rohingya bayan da aka gano gawar mutane 10 a rami guda.

Wata sanarwa da ofishin rundunar sojin kasar Myanmar ta fitar ta bubar da cewa sojojin sun amsa zargin kashe Musulmin Rohingya 10 marasa rinjaye da ke jihar Rakhine bayan faruwar lamarin a watan Satumban shekarar 2017. Sai dai rundunar ta ce akwai hannun wasu mazauna kauyen Inn Din a kisan da ake zargin sojojin da aikatawa.

A baya dai sojojin sun sha musanta rahotannin shafukan sada zumunta da ke alakanta su da kisan, inda suka ce sun kashe Musulmin ne a matsayin 'yan ta'addan kabilar Rohingya.