Cutar Ebola ta sake bullowa a Kasar Guinea
March 18, 2016Talla
Kakakin mai Magana da yawun hukumar yaki da cutar a kasar Ibrahima Syalla ya fada a ranar alhamis din nan cewar, cutar ta kunno kai ne daga gidan wasu iyalai a Koropara da ke da nisan kilomita dubu daya da Conakry babban birnin kasar, a inda ya kara da cewar a kwai yiwuwar Karin samun mutane uku masu dauke da kwayar cutar ta Ebolan.
Kazalika Ibrahima Syalla ya ce tuni hukumomin lafiyar kasar Guinean suka fara daukar matakan dakile bazuwar cutar zuwa wasu yankunan kasar.
Hukumomin da ke yaki da cutar hade da ministan harkokin lafiyar tuni suka kira wani taron gaggawa domin duba yadda zasu tinkarin yadda za a dakile cutar da yanzu haka ke barazana ga al'ummar kasar.