Cutar Ebola na kara yin barazana a duniya | Labarai | DW | 30.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cutar Ebola na kara yin barazana a duniya

Cutar Ebola tana ci gaba da barazana wa kasashen yankin yammacin Afirka

Fargaba na kara karuwa sakamakon barazanar yaduwar cutar Ebola mai saurin kisa daga yammacin Afirka zuwa nahiyar Turai. Kasashen na turai dai na gargadin cewa cutar ta gagari kwandila kuma tana iya yaduwa inda rahotanni ke nuni da cewa kungiyar Tarayyar Turai wato EU ta ba da gudunmawar kudade masu tsoka domin taimakawa wajen yaki da cutar. Kungiyar likitoci na gari na kowa, wato Doctors Without Borders (Medical San Frontier) ke gargadin cewa cutar da ke kara kamari a kasashen Guinea da Liberiya da kuma Salo ka iya kara yaduwa zuwa sauran kasashe.

Tuni dai wasu kamfanonin jiragen sama da suka hadar da pan-African airline ASKY suka dakatar da zirga-zirgar jiragensu daga ko kuma zuwa Liberiyan. Cutar ta hallaka wani fitaccen likita da ke kan gaba wajen ba da taimako a yakin da ake da cutar a kasar Saliyo mai suna Dr. Sheik Umar Khan.

Mawallafi: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Suleiman Babayo