1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Brazil: Mutum 751 sun mutu cikin sa'oi 24

Abdullahi Tanko Bala
May 9, 2020

Yawan mutanen da suka rasu a sakamakon annobar corona a duniya baki daya ya karu zuwa kusan mutane dubu 275 yayin da wasu mutanen fiye da miliyan uku da dubu dari tara suka kamu da kwayar cutar.

https://p.dw.com/p/3bxz8
Brasilien Coronavirus Massengrab in Manaus
Hoto: picture-alliance/dpa/C. Batata

Kasar Brazil wadda ta fi fuskantar annobar a tsakanin kasashen kudancin Amirka ta ruwaito karuwar mutane 751 da suka rasu wanda ya kawo adadin mutanen da suka rasu a kasar zuwa kusan mutum 10,000

A kasar Italiya yawan wadanda suka rasu ya haura dubu talatin yayin da aka sami sabbin kamun cutar da suka kai 243 a fadin kasar. Kasashen Amirka da Birtaniya sune suka fi yawan wadanda suka rasu a sakamakon cutar ta corona.

A waje guda kuma hukumar lafiya ta duniya ta sanar da gibin dala biliyan daya da miliyan dari uku daga cikin dala biliyan daya da miliyan dari bakwai da ta ke bukata domin aiwatar da kokarin da ta ke yi na yaki da annobar ta COVID 19.

Sanarwar na zuwa ne jim kadan bayan Amirka ta janye tallafin da ta ke bayarwa ga hukumar lafiyar ta duniya WHO.