Covid 19: Erdogan da Trump sun tattauna | Labarai | DW | 23.05.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Covid 19: Erdogan da Trump sun tattauna

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da takwaransa na Amirka Donald Trump sun kara jaddada shirinsu na hada kai domin yaki da cutar Covid 19 da kyautata dangantakar diplomasiya tsakanin kasashensu.

Wata sanarwa da ofishin shugaban na Turkiyya ta fidda ta ce shugabannin biyu sun aminta kan hakan ne bayan da suka yi wata zantawa ta wayar tarho, kuma baya ga batun yaki da corona sun kuma tabo batun rikicin kasar Siriya da na Libiya inda suka amince da ci gaba da hulda a siyasance da kuma ta fannin aikin soja da zummar samar da zaman lafiya. 

Zantawar shugabannin biyu dai na zuwa ne daidai lokacin da Turkiyyan ke samun raguwar mace-macen da ke da nasaba da annobar COVID-19 wanda hakan yasa ministan sufurin kasar ya sanar da cewar za a maido da sufurin wasu jiragen kasa a kasar domin ci gaba da harkokin yau da kullum a ranar 28 ga wannan wata da muke ciki.