1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Covid-19 da masu tabin kwakwalwa

May 21, 2020

Annobar coronavirus da fargabar kamuwa da ita na iya haddasa rashin lafiyar tabin hankali ga jama'a masu rauni a kwakwalwa.

https://p.dw.com/p/3ca5P

A yayin da cutar Coronavirus ke cigaba da kasancewa babban kalubale ganin yadda ake cigaba da kashe kudi wajen sayen naurorin gwaji da ma samar da wajejen kula da wadanda suka kamu da cutar. A Ostraliya, akwai wadanda ke fama da damuwa irin wanda ake fargaban idan ba a dauki mataki da wuri ba zai kai ga tabin hankali. Don haka ne ma Firaministan kasar Scott Morrisson da majalisar ministocinsa sun ware wani kaso na kudi dan tabbatar da lafiyar kwakwalwar jama’a sakamakon yawan fargaba da dimuwar da yaduwar cutar ta janyo wa jama’a.