1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yuwuwar warware takun saka tsakanin Mali da Cote d'Ivoire

Suleiman Babayo LMJ
October 7, 2022

Kasar Cote d'Ivoire ta nuna cewa ana gab da kawo karshen takun saka da ke faruwa da kasar Mali kan kama wasu sojojin kasar 46 kimanin watanni uku da suka gabata.

https://p.dw.com/p/4HupN
hada hotunan Shugaba Assimi Goïta na Mali da Shugaba Alassane Ouattara na Cote d'Ivoire
Shugaba Assimi Goïta na Mali da Shugaba Alassane Ouattara na Cote d'Ivoire

A wannan Jumma'a Shugaba Alassane Ouattara na kasar Cote d'Ivoire ya nuna yuwuwar samun mafita kan takaddama da mahukuntan kasar Mali, inda ake tsare da sojojin kasar 46 tun kimanin watanni uku da suka gabata. Shugaba Ouattara ya fadi haka lokacin ganawa da Shugaba Umaro Sissoco Embalo na kasar Guinea-Bissau wanda yake jagorancin kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS.

Tun farko Shugaban Cote d'Ivoire ya gana da Shugaba Faure Gnassingbe na Togo mai shiga tsakani bisa takaddamar.

Tun ranar 10 ga watan Yuli aka cafke sojojin na Cote d'Ivoire lokacin da suka isa filin jiragen saman birnin Bamako na kasar Mali, inda Cote d'Ivoire ta ce suna cikin tawogar dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, amma gwamnatin Mali karkashin Kanar Assimi Goita ta ce sojojin haya ne da za su hargitsa zaman lafiya, abin da ya haifar da takun saka tsakanin kasashen biyu.